Ketare

Za a iya sauya gwamnati a Iran idan ba ta yi abin da ya dace ba – Trump

Donald Trump ya yi wasu kalamai da ke nuni da yiwuwar samun sauyin shugabanci a Iran.

Shugaban na Amurka ya ce duk da cewa ba daidai ba ne a siyasance a yi amfani da kalmar sauya gwamnati, amma idan har gwamnatin Iran mai ci ba ta iya – abin da ya kira sake mai do da martabar Iran – to me zai hana a samu sauyi.

Kalaman mista Trump sun ci karo da na jami’an gwamnatinsa waɗanda tun bayan harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran ,su ke ta nanata cewa Amurka ba ta da muradin tsige shugabannin Iran.

Akwai dakarun Amurka guda dubu arba’in a sansanoni daban daban da ke yankin gabas ta tsakiya wanda halin yanzu ke cikin shirin ko ta kwana yayin da Amurka ke tsammanin martani daga Iran.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta gargaɗi Amurkawa da ke fadin duniya da su yi taka tsan-tsan a duk inda suke

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button