Labarai
Gwamnatin Tarayya ta ce yanzu haka akwai tituna, gadoji da manyan ayyuka sama da 420 da ko dai ta kammala su ko kuma tana dab da gamawa a shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Shugaban kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattawa, Sanata Barinada Mpigi ne ya sanar da hakan yayin da yake jawabi a taron Hukumar da ke Kula da Ayyukan Injiniyoyi ta Najeriya (COREN) karo na 33 a Abuja ranar Talata.
Sanatan, wanda Ashley Emenike ya wakilta, ya kuma yaba wa injiniyoyin, wadanda ya bayyana a matsayin ginshikin ci gaban tattalin arzikin kasa da kuma ayyukan raya kasa.
Sai dai Sanatan ya nuna damuwa kan yadda ya ce ana yawan samun matsaloli a wasu ayyukan da injiniyoyin ke yi kamar su rushewar gine-gine, lalacewar hanyoyi da sauran ayyuka, inda ya alakanta hakan da rashin bin ka’idojin aiki a lokacin da ake gina su.




