Labarai

Yaushe rashin tsaro zai zo karshe Nijeriya?a?

Wani rahoto da kungiyar kasa da kasa ta The International Society for Civil Liberties and Rule of Law ta fitar ne, ya nunar da cewa akwai sassa 950 cikin surkukin dazuzzukan yankin Kudu maso Gabashin Najeriya da ‘yan fashin daji da masu satar mutane da Fulani makiyaya ke a bobboye suna aikata muggan laifuka na tayar da zaune tsaye

Kungiyar ta Int’l Soc For Civil Liberties and Rule Of Law, ta kuma zargi gwamnonin yankin da nuna halin ko in kula

Kungiyar ta kasa da kasa ta ce daga cikin laifukan da awadannan miyagu ke aikatawa a dazuzzukan Najeriya, har da kisa da kai farmaki kan jama’a

To sai dai fa kuma Barista Abdullahi Jalo da ya kasance Bafulatani, ya wanke Fulanin Najeriyar da shiga cikin jerin wadanda ake magana na aikata mugagn laifuka a yankin na Igbo.

A wani labarin kuma bayanai daga rundunonin tsaron soji da na jami’an tsaro na farin kaya DSS a kasar suka nunar da cewa sun kama wata babbar mota makare da makamai da aka yi niyyar kai su ga sansanin ‘yan rajin kafa kasar Biafra na kungiyar IPOB a yankin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button