Laifukan cin zarafin ɗan adam a Darfur na Sudan na ƙara ta’azzara a cewar Mataimakin mai gabatar da ƙara na kotun ICC

Wani babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ya bayyana cewa akwai “dalili masu yawa da za a yarda cewa ana aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama” a yankin Darfur da ke yammacin Sudan da yaki ya daidaita.
Mataimakiyar Mai Gabatar da Kara ta ICC, Nazhat Shameem Khan, ta gabatar da hakane a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis kan rikicin mai tsanani, wanda ya yi kamari tun daga shekarar 2023, inda ya kashe fiye da mutane 40,000 kuma ya raba mutane miliyan 13 da muhallansu.
Khan ta ce girman wahalhalu da rikicin a Darfur ya kai matsayin da ba za a iya bayyanawa ba, inda yunwa ke kara ta’azzara, ana kai hari ga asibitoci, ayarin motocin agaji da sauran kayayyakin more rayuwa na farar hula.
Ta ce yana da “wahala a samu kalmomi da suka dace don bayyana irin wahalar da ake ciki a Darfur.
A cikin watan Yuni, Hukumar Bincike Mai Zaman Kanta ta Majalisar Dinkin Duniya don Sudan ta yi gargadin cewa duka Rundunar Sojojin Sudan (SAF) da dakarun sa kai na Rapid Support Forces (RSF) sun ƙara amfani da manyan makamai a wuraren da jama’a ke zaune kuma sun mayar da agajin jin kai makami, a yayin mummunan sakamakon yakin basasa.
Babban mai gabatar da kara na ICC, Karim Khan, ya shaida wa Kwamitin Tsaro a watan Janairu cewa akwai dalilai da ke nuna cewa duka bangarorin biyu na iya aikata laifukan yaki, laifukan cin zarafin bil’adama ko kisan kare dangi a yankin, yayin da gwamnatin tsohon Shugaban Amurka Joe Biden ta yanke shawarar cewa RSF da wakilanta suna aikata kisan kare dangi.




