Labarai
Kungiyar Manoma ta kasa ta ce idan noma ya lalace a Najeriya to shugaban kasa Bola Tinubu shi ne sila.

Kungiyar manoman ta bayyana damuwa kan yadda shinkafa da masara daga kasashen waje ke mamaye kasuwannin cikin gida, lamarin da suka ce na barazana ga cigaban noma a kasar nan.
Manoman sun bayyana hakan ne a sakonnin da suka wallafa a shafin sada zumunta na X, inda suka zargi manufar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da kawo cikas ga noman cikin gida.
Sun ce saukin harajin shigo da kayan abinci da gwamnatin tarayya ta bayar ya janyo faduwar farashin kayan abinci, amma hakan yana cutar da masu noma a gida.




