Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta yi korafin cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta mayar da yankin saniyar ware a kasafin ayyukan raya kasar da take yi a Najeriya.

Da yake jawabi yayin wani taron tattaunawa da ’yan kasa da Gidauniyar Tunawa da Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna ranar Talata, Shugaban Kwamitin Amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu (Wazirin Dutse), ya yi zargin cewa ana nuna wa yankin bambanci a muhimman manufofin gwamnati da kuma aiwatar da ayyukan raya kasa.
ACF ta ce hakan na faruwa ne duk da irin irin tarin gudunmawar da yankin ya ba gwamnatin mai ci a zaben 2023 da ya gabata.
Taron dai mai taken: “Nazarin alkawuran zabe: Inganta alakar gwamnati da ’yan kasa domin hadin kan kasa” ya tara gwamnoni da manyan masu rike da mukaman Gwamnatin Tarayya, ciki har da ministoci da sarakunan gargajiya da kuma kungiyoyin fararen hula.
A cewar wadanda suka shirya taron, an shirya shi ne domin karfafa fahimtar juna tsakanin mahukunta da kuma mutane a fadin arewacin Najeriya.




