Jam’iyyar APC za ta san ta yi kuskure game da sauke tsohon shugaban bata wato Abdullahi Umar Ganduje cewar Aminu Dahiru Ahmad

Wani hadimin tsohon shugaban jam’,iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje wato Aminu Dahiru Ahmad ya ce jam’iyyar za ta gane ta yi kuskure kan saukarsa daga shugabancin.
A wata doguwar wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana takaicinsa kan rashin nuna wa Ganduje halasci, duk da irin ci gaban da ya kawo jam’iyar wanda ya ce ba a taba samun makamancinsa ba.
Aminu ya ba da misali da yadda aka dinga tururuwar shiga APC a lokacin mulkin Ganduje da kuma yadda Gwamnoni suka dinga sauya sheka, wanda ya ce ko hakan ya isa ya nuna kwarewarsa a fagen siyasa.
A wani sakon da ya wallafa kafin wasikar, ya ce za su rama biki idan lokaci ya yi, kuma a nan ne za a gane Ganduje shi ne rufin asirin APC.
Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ne Ganduje ya ajiye muƙaminsa na shugabancin jam’iyyar APC.



