Labarai

‘Matsaloli sun yi wa Yammacin Afirka ɗaurin goro’

Shugabannin ƙasashen yammacin Afirka da suka yi wani taro a Najeriya sun ce yankin na fuskantar barazanar ta’addanci da sauyin yanayi da juyin mulkin soja da kuma talauci.

Taron Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afrika ta ECOWAS wanda aka kammala jiya Lahadi ya yi gargadi kan matsalolin masu hatsari.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce rashin tabbacin siyasa da safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma laifukan da suka shafi kasashe da dama na nufin lokaci ya yi da za a sake gyara tsarin tsaro na haɗin gwiwa a yankin.

Kungiyar dai ta fuskanci babban ƙalubale a farkon wannan shekara bayan ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da ke ƙarƙashin mulkin soja a halin yanzu suka fice daga cikinta, inda suka kafa nasu ƙawancen ƙasashen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button