Labarai

Jam’iyyar NNPP, ta bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yi mata takarar shugaban ƙasa a 2023, ba zai tsaya takara a 2027 ba.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dokta Agbo Major, ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya mayar da martani kan wata magana da Buba Galadima ya yi.

Galadima, ya ce har yanzu Kwankwaso yana cikin NNPP kuma zai tsaya takara a 2027.

Amma shugaban jamiyyar ya bayyana cewa tafiyar NNPP da Kwankwasiyya ta ƙare tun bayan zaben shugaban ƙasa na 2023.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button