Labarai

A yau ne majalisar dinkin duniya ke cika Shekara 80 da kafuwa.

Shekara 80 da suka gabata a makamanciyar wannan rana, an rattaba hannu kan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a San Francisco, inda aka sauya tsari na yaki da duniya ta fuskanta shekaru da dama zuwa samar da kyakkyawar makoma.

Tsawon shekaru 80, Majalisar ta tsaya a matsayin mai bayyana fatanmu na hadin gwiwar kasa da kasa, mai bayyana ma’anar burin na kawo karshen “cutarwa a yaki.”

Majalisar ta kasance kungiya daya tilo da bata da tamka, kuma ita kadai ce ta dawwama.

Wannan tsayin daka yana da ban mamaki idan aka yi la’akari da yanayin kafuwarta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button