Hukumar KASITDA ta ci alwashin bunƙasa gudanar da mulki ta amfani da fasahar zamani a Kano

Hukumar bunƙasa fasahar zamani ta jihar Kano (KASITDA) ta sake jaddada kudurinta na bunkasa tsarin tafiyar da gwamnati ta hanyar amfani da fasahar zamani a jihar Kano, bayan wata ziyarar aiki da ta kai hukumar raya birane ta KNUPDA.
Babban daraktan hukumar, Bashir Abdu Muzakkari, ya bayyana cewa ziyarar na da nufin gabatar da wata sabuwar manhajar kwamfuta da aka kirkira domin inganta ayyukan tsara birane, daidai da ajandar sauyi zuwa fasahar zamani ta jihar Kano.
Ya ce shirin wani bangare ne na kokarin KASITDA na gaggauta sauya tsarin aiki zuwa na fasahar zamani a muhimman bangarori kamar lafiya, shari’a da kuma harkokin filaye.
A cewarsa, wannan tsari zai taimaka wajen maye gurbin tsohon tsarin takardu da na zamani, wanda zai kara sauri, inganci da saukin samun ayyukan gwamnati ga al’ummar jihar Kano.
Dr. Muzakkari ya kara da cewa shirin zai inganta bin dokokin tsara birane, kara gaskiya da tsaro a harkokin gwamnati, tare da habaka kudaden shiga na cikin gida.
Ya kuma bayyana cewa a bangaren shari’a da filaye, tsarin zai saukaka tafiyar da shari’o’i da kula da filaye, yayin da a bangaren lafiya zai taimaka wajen daidaita bayanan marasa lafiya da inganta tsare-tsaren kiwon lafiya.
A karshe, ya ce wannan shiri zai kara amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati, rage tsaiko a ayyuka, da kuma samar da ingantaccen tushe na bunkasa tattalin arziki da kirkire-kirkire a jihar Kano.




