An fitar da Trump daga taron manema labarai bayan harbe-harbe a Washington

An yi gaggawar fitar da shugaban Amurka, Donald Trump, daga wurin taron White House Correspondents’ Dinner da aka gudanar a otal ɗin Washington Hilton, bayan da wani mutum ɗaya ya harba bindiga a cikin zauren taron a daren
Rahotanni sun ce mahalarta taron sun rika boyewa a ƙarƙashin tebura da sauran wurare yayin da aka ji ƙarar harbe-harbe a cikin zauren.
Wani jami’in tsaron sirri ya samu rauni daga kusa, amma rigar kariya daga harsashi ta ceci rayuwarsa.
An tsare mutane da dama a cikin zauren na kusan awa guda kafin jami’an tsaro suka tabbatar da tsaron wurin.
Shugaban ya bayyana cewa an kama wanda ake zargi a wurin da ya aikata laifin, yana mai yabawa jami’an tsaron sirri da suka cafke shi. An gano sunan wanda ake zargin da Cole Tomas Allen mai shekaru 31 daga jihar California, kuma ana sa ran gurfanar da shi a kotu ranar Litinin.
Rahotanni sun ce Allen bako ne a otal ɗin kuma malami ne na wucin gadi a California.
Wannan lamari na zuwa ne bayan wani makamancin harin a shekarar 2024, lokacin da aka kai hari a wani gangamin siyasa a Pennsylvania, inda Trump ya samu rauni a kunnen sa bayan harbe-harbe.




