Ketare
Mun sauya salon yaƙinmu daga kare kai zuwa zafafa hare-hare – Iran

Babban kwamandan shlkwatar rundunar sojin Iran da ake yi wa laƙabi da Khatam al-Anbiya ya ce ‘salon’ yaƙin ƙasar ya sauya daga kare kai zuwa ƙaddamar da hare-hare.
”Don haka mun sauya salon yaƙin dakarunmu da ke filin daga”, in ji shi.
Kafofin yaɗa labaran Iran, sun ce Manjo Janar Abdollahi ya ce tuni ƙasar ta ”ƙera sabbin makamai na zamani”, waɗanda da su ya ce za su wargaza shirin waɗanda ya kira ”maƙiya”.




