Ketare
An dakatar da sauka da tashin jirage a Dubai

Hukumomi a Dubai sun sanar da tsagaita sauka da tashin jirage na wani ɗan lokaci “domin tabbatar da lafiyar fasinjoji da ma’aikata”.
Kafin nan dai an rahotanni sun ce ma’aikatan agajin gaggawa sun yi fama da wata wuta da ta tashi a filin mai alaƙa da harin jirgi maras matuƙi da ya lalata tankin mai.
An nemi fasinjoji da su nemi bayanan sauka da tashinsu daga wurin kamfanonin da suke hulda da su.
Kafin dai fara yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan Iran, filin jirgin saman na Dubai shi ne wanda ya fi kowanne hada-hadar sauka da tashin jirage a duniya inda fasinjoji miliyan 90 suka yi amfani da filin a 2025.



