Labarai

Sojoji sun kashe kasurgumin dan binidiga da ya shahara a Tiktok mai suna Alti

Dakarun sojin Najeriya sun kashe wani kasurgumin kwamandan ‘yanbindiga da aka fi sani da Alti, wanda ake zargi da addabar yankunan da ke kan hanyar Gusau zuwa Funtua da sauran yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya.

 

Wata majiya daga hedikwatar sojoji ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) cewa an kashe Alti ne a wani samame na soji da aka kai kwanan nan, lamarin da ake ganin babbar illa ce ga ƙungiyoyin ‘yanbindiga a jihohin Zamfara da Katsina da kuma wasu sassan jihar Sokoto.

 

Rahotanni sun nuna cewa duk da ƙarancin shekarunsa, Alti ya zama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ‘yan bindiga a yankin, inda ake zargin yana gudanar da sansanoni daga kudancin Gusau har zuwa yankunan Jibiya da Funtua.

 

Daga waɗannan wurare, mayaƙansa na kai hare-hare tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa, kai farmaki a hanyoyi, har ma da amfani da bama-bamai na IED a manyan tituna.

 

An kuma bayyana cewa Alti ya shahara a tsakanin ‘yan bindiga da lakabin “bankin kuɗi” saboda yadda yake sarrafa kuɗaɗen fansa daga sace-sacen mutane, tare da bayyana a bidiyoyin TikTok yana nuna makamai da yin barazana.

 

Masana harkokin tsaro sun ce kashe Alti na iya rage ayyukan sace-sacen mutane a yankin Zamfara zuwa Katsina, tare da raunana ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ke biyayya gare shi.

 

Al’ummomin yankin dai sun dade suna fama da hare-hare da garkuwa da mutane, inda galibi ake biyan kuɗaɗen fansa masu yawa, abin da ya sa kashe manyan shugabannin ‘yan bindiga kamar Alti ke da muhimmanci wajen dawo da zaman lafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button