Umar Haruna Doguwa Na Dab da Zama Shugaban APC na Kano

Bayanai daga majiyoyin siyasa sun nuna cewa ɓangaren Gwamna Abba Kabir Yusuf sun amince da tsayar da Umar Haruna Doguwa a matsayin sabon Shugaban APC na Jihar Kano, a zaɓen da ake sa ran gudanarwa bayan ƙarfe 8 na dare a filin wasa na Sani Abacha Stadium.
Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa ɓangaren tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, sun amince da Muntari Ishaq a matsayin sabon sakataren jam’iyyar.
Sai dai a wani ɓangare, ana cewa Sanata Barau Jibrin na goyon bayan Alhaji Baba domin ya zama sabon sakataren jam’iyyar, lamarin da ke nuna yiwuwar takara mai zafi a cikin gida.
Idan za a tuna, Doguwa ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban APC na Kano kafin a kawo Abdullahi Abbas a lokacin rikicin siyasa tsakanin Rabiu Musa Kwankwaso da Ganduje, inda a wancan lokaci Doguwa ya mara wa Kwankwaso baya.
Ana kallon wannan zaɓe a matsayin wani muhimmin mataki gabanin fara kakar siyasar 2027, inda ake sa ran za a fara zaɓen Shugaban ƙasa da ’yan majalisar tarayya tun daga watan Janairu mai zuwa.




