Iran Ta Ce Ta Shirya Wa Dogon Yaƙi Da Amurka

Sakataren Majalisar Tsaron Iran, Ali Larijani, ya bayyana cewa ƙasarsa a shirye take domin gwabza yaƙi mai tsawo da Amurka idan hakan ta taso.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Larijani ya ce Iran ba ta taɓa tsokano faɗa ba a cikin fiye da shekaru 300, yana mai jaddada cewa dakarun sojin ƙasar ba sa shiga yaƙi sai domin kare kai.
“Duk abin da zai faru, za mu kare kanmu, kuma za mu yi amfani da kafuwar daularmu ta tsawon shekaru 6,000 don tabbatar da cewa maƙiya ba su samu nasara a kanmu ba,” in ji shi.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan da sakataren tsaron Amurka ya bayyana a wani taron manema labarai cewa harin da Amurka ta ƙaddamar kan Iran ba na dindindin ba ne.
A cewarsa, manufar harin ita ce lalata makaman linzami na Iran, da rundunar sojin ruwanta, tare da wasu muhimman kayayyakin sojin ƙasar.
Sabbin bayanan na nuna yadda takun-sakar ke ƙara ƙamari tsakanin ɓangarorin biyu, lamarin da ke janyo hankalin duniya kan yiwuwar rikici mai tsawo a yankin.




