Shawarwari Kan Amfani da Wayoyi da Kafafen Sada Zumunta a Watan Ramadan

An shawarci al’ummar Musulmi da su tsara yadda za su riƙa amfani da wayoyinsu da kafafen sada zumunta a cikin watan Ramadan, domin kada hakan ya zama sanadin rage musu lada ko shagaltar da su daga ibada.
ya kamata Musulmi su gyara niyya tun daga farko, su tabbatar da cewa duk abin da za su kalla ko su wallafa yana ƙara musu kusanci ga Allah, ba rage lada ba.
Ramadan wata ne na azumi, sallah, karatun Al-Qur’ani, zikiri da istighfari, don haka ya dace a mayar da amfani da waya wata hanya ta taimakawa ibada.
Haka kuma, an bukaci a sanya tsari da iyaka wajen amfani da waya, kamar kayyade lokaci na musamman don lilo a kafafen sada zumunta, tare da rage amfani da data da kashe sanarwar (notification) na manhajojin da ba su da muhimmanci.
An kuma ba da shawarar guje wa amfani da waya a lokutan ibada kamar bayan sahur zuwa sallar asuba da kuma lokacin sallar tarawihi.
Shawarwarin sun ja hankali kan gujewa kallon abubuwan batsa, tsegumi, cece-kuce marasa amfani, da yada labarai ba tare da tabbatar da sahihancinsu ba, domin azumi ba wai daina cin abinci kaɗai ba ne, har da nisantar munanan ɗabi’u.
An kuma ƙarfafa gwiwar Musulmi da su maida kafafen sada zumunta wurin yada alheri ta hanyar sauraron tafsiri da hadisi, karatun Al-Qur’ani ta manhajoji, da tura saƙonnin nasiha masu amfani, maimakon zama hanyar yada fitina.
Haka zalika, an shawarci iyaye da su sanya dokoki kan yadda ‘ya’yansu za su riƙa amfani da waya, musamman domin kada hakan ya hana su tashi sahur ko halartar sallar asuba.
A ƙarshe, an tunatar da cewa waya na iya zama hanya zuwa samun lada da Aljanna ko kuma akasin haka, don haka ya kamata a yi amfani da ita cikin hikima, musamman a wannan wata mai albarka da kwanaki kaɗan ne.




