Saudiyya Ta Shirya Bai Wa Miliyoyin Raƙuma Fasfo Domin Inganta Kula da Su

Ƙasar Saudiyya ta sanar da shirinta na fara bai wa miliyoyin raƙuman da ke ƙasar fasfo, a wani mataki da aka ce zai taimaka wajen inganta kula da su da kuma sauƙaƙa tsarin gudanar da muhimmin fannin kiwon raƙuma.
Jami’an gwamnati sun bayyana cewa wannan tsari zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin fannin, da inganta ingancin kiwo, tare da samar da sahihin kundin bayanai da za a dogara da shi wajen tantance mallaka da shaida ta raƙuma.
Wani saƙo da Ma’aikatar Muhalli, Ruwa da Noma ta wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna hoton fasfon raƙuma, wanda ke da launin kore, dauke da tambarin ƙasar Saudiyya da kuma hoton raƙumi mai launin zinariya.
A cewar bayanan gwamnati, a shekarar 2024, an ƙiyasta cewa akwai kusan raƙuma miliyan 2.2 a faɗin ƙasar Saudiyya.
Saudiyya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke ba raƙuma muhimmanci sosai, inda har ta kan shirya gasar kyawun raƙuma a lokacin bukukuwan shekara-shekara, abin da ke nuna rawar da raƙumi ke takawa a al’adu da tattalin arziƙin ƙasar.




