GWAMNATIN BAUCHI TA GANO MA’AIKATAN BOGI FIYE DA DUBU 3, A JIHAR

Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana cewa ta gano tare da cire ma’aikatan bogi sama da dubu uku da ke karɓar albashin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya ceto kuɗaɗen jihar sama da naira biliyan 4.16.
An bayyana hakan ne a wani taro na musamman na Kwamitin Kula da Tattalin Arzikin Jihar, wanda Gwamna Bala Mohammed ya jagoranta a Fadar Gwamnati da ke Bauchi.
Bayan kammala taron, Shugaban Ma’aikatan Jihar Bauchi, Muhammad Sani Umar, tare da Babban Mashawarcin Tattalin Arziki ga gwamna, Yahuza Adamu Ningi, sun shaida cewa an sake duba tsarin biyan albashi gaba ɗaya domin tabbatar da gaskiya da inganci.
A cewar Yahuza Adamu Ningi, an gudanar da aikin tantance ma’aikata da albashi ne tare da kamfanin Onyx Investment Advisory Limited, wanda hakan ya kai ga gano tare da cire ma’aikatan bogi.
Ya ƙara da cewa sabon tsarin ya ceci naira biliyan 4.16 tun bayan fara aiwatar da shi a watan Agustan 2024.
A wani ɓangare kuma, Muhammad Sani Umar ya bayyana cewa kwamitin ya amince da biyan alawus na wata-wata ga limaman masallatan Juma’a da fastocin coci-coci a faɗin Jihar Bauchi, ba tare da la’akari da mazhaba ko addini ba, a wani yunkuri na ƙarfafa haɗin kai da walwalar addinai.




