Labarai
Gwamnatin Jihar Kano Ta Nemi Mataimakin Gwamna, Aminu Abdulsalam, Ya Yi Murabus

Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da ya gaggauta yin murabus daga mukaminsa.
Wannan kira na zuwa ne kamar yadda Kwamishinan yada labarai na jihar ya bayyana.
Sai dai, kawo yanzu, ba a bayyana dalilin da ya sa gwamnatin ta bukaci ya sauka daga mukamin nasa ba.


