Labarai

An Kama Wani Sojan Gona Yana Satar Babura a Kano Da Sunan Jami’in FRSCD

Rundunar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), reshen jihar Kano, ta sanar da kama wani mutum mai suna Abdullahi Ali, mazaunin ƙauyen Bela a ƙaramar hukumar Ungogo, bisa zargin satar babura da kuma yin amfani da sunan jami’in FRSC domin aikata laifuka a faɗin jihar Kano.

Kamar yadda wata sanarwa daga Kwamandan Sashen na FRSC a Kano, CRC Abdullahi Labaran SPEO, ta bayyana, an kama wanda ake zargin ne a ranar 19 ga watan Janairun 2025, biyo bayan ƙorafi da yawa daga al’umma a wurare daban-daban na jihar Kano.

ƙorafin ya shafi ayyukan wasu ƴan daba ne da ke yin sojan gona da sunan jami’an FRSC, inda suke kama babura ba bisa ƙa’ida ba da sunan gudanar da aikin sintiri.

Bayan samun ingantattun bayanai na sirri, jami’an sashin leƙen asiri na FRSC sun yi nasarar kama Abdullahi Ali, wanda ake zargi da aikata waɗannan laifuka.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin yana kwace babura ne da ƙarfi yayin da yake nuna kansa a matsayin jami’in FRSC, kuma ana zargin cewa wasu daga cikin baburan da ya kama an sace su

Sanarwar ta ƙara da cewa, “A lokacin da aka kama shi, an gano wata lasisin tuƙi ta bogi a hannunsa, wanda hakan ya ƙara tabbatar da cewa yana amfani da shaidar ƙarya ne don sauƙaƙa ayyukan aikata laifuka.”

An mika wanda ake zargin zuwa ofishin ƴansanda na Gwale, domin gudanar da ƙarin bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.

Gargadi Ga Jama’a

Rundunar ta FRSC ta bayyana a fili cewa Abdullahi Ali ba ma’aikacinta ba ne, kuma ta shawarci jama’a da su kasance a Ankare tare da kai rahoton duk wani mutum da suke zargi wanda ya nuna kansa a matsayin jami’in

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button