Siyasa
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Ya Gana da Shugaba Tinubu a Abuja

A ranar Litinin, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar aiki ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Wannan ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta yada jita-jitar cewa gwamnan na shirin sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
Ziyarar ta kara rura wutar wannan hasashe, inda ake ganin tattaunawar a matsayin wani mataki na karshe na kammala shirin ficewar Gwamna Yusuf daga jam’iyyar NNPP.
Wannan batu na sauya sheka ya haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Kano, inda wasu manyan jagororin jam’iyyar NNPP, ciki har da jagoran jam’iyyar na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, suka nuna adawarsu ga wannan yunkuri.




