Ketare

Mutane biyu sun mutu sakamakon harbin da ƴansanda suka yi kan masu zanga-zanga a kasar Kenya.

Ƴansandan sun buɗe wuta ne kan ayarin wasu masu zanga-zanga a babban birnin Nairobi, na ƙasar.

Jami’an ƴansandan sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye tare da toshe hanyoyi domin hana jama’a isa tsakiyar birnin.

An shirya gudanar da zanga-zangar ne a faɗin ƙasar domin tunawa da fara zanga-zangar neman mulkin dimukradiyya a 1990.

Masu fafutikar kare haƙƙin bil’adama sun zargi gwamnati da tura wasu ƴandaba da ta ɗauka haya domin lalata zanga-zangar baya-bayan nan, zargin da hukumomin tsaron suka musanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button