Sarkin Kaltungo Ya Jaddada Kudirinsa na Wayar da Kan Al’umma Kan Zaman Lafiya

Mai Martaba Sarkin Kaltungo, Engr. Saleh Muhammad Umar OON, Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakuna da Hakimai ta Jihar Gombe, ya bayyana kudirinsa na ci gaba da wayar da kan al’ummar Masarautar Kaltungo kan muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar bakoncin sabon Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, wanda ya kai masa ziyara tare da tawagarsa a fadar masarauta.
Mai Martaba Sarkin Kaltungo ya tabbatar da cewa masarautarsa za ta ci gaba da hada kan al’umma ba tare da la’akari da bambancin addini, kabila ko al’adu ba, tare da bayar da ilimi, tallafawa matasa da kuma bunkasa zaman lafiya a dukkan fannoni.
Da yake nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya bayyana cewa ya zabi fara rangadin aikinsa ne daga Masarautar Kaltungo, sakamakon yadda yankin ke ci gaba da morewa zaman lafiya duk da bambancin addinai, kabilu da al’adu da ke cikinsa.
CP Umar ya jaddada aniyar rundunar ’yan sanda na hada kai da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki domin karfafa tsaro da tabbatar da zaman lafiya a fadin Jihar Gombe.
Ya kuma bukaci matasa da su rungumi zaman lafiya, su nemi sana’o’i masu amfani, tare da gujewa shaye-shaye da duk wani abu da zai iya jefa su cikin aikata laifi.




