Ɗan Kasuwa a Kano Ya Taya Gwamna Abba Kabir Yusuf Murnar Cika Shekaru 63, da aihuwa Yakuma Yaba da Ayyukan Gwamnatinsa

Wani fitaccen ɗan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji Gambo Haruna Yusuf, ya taya Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, murnar cika shekaru 63 masu albarka, inda ya yabawa gwamnan bisa salon shugabanci da ayyukan alheri da gwamnatin sa ke aiwatarwa a fadin jihar.
Alhaji Gambo Haruna Yusuf, wanda aka fi sani da Gambo Kura, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da ’yan jarida a yammacin wannan rana a Kano. A jawabin nasa, ya bayyana kansa a matsayin masoyin gwamna kuma mai bibiyar ayyukan gwamnatin Kano, yana mai cewa babu shakka al’ummar jihar sun gamsu da irin ci gaban da suke gani a wannan gwamnati.
A cewarsa, gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta kawo sauye-sauye masu ma’ana a fannoni daban-daban, musamman a bangaren ilimi, lafiya, raya kasa da walwalar jama’a, wanda hakan ya kara samun karbuwa da goyon bayan al’umma.
“Gwamna Abba Kabir Yusuf shugaba ne mai kishin jama’a, mai hangen nesa da jajircewa wajen ganin al’ummar Kano sun more ribar dimokuradiyya. Ayyukan alherin da wannan gwamnati ke yi sun tabbatar da cewa an zo da gaske domin yi wa jama’a aiki,” in ji Alhaji Gambo Kura.
Ya kara da cewa, a matsayinsa na ɗan kasuwa kuma ɗan jihar Kano, yana ganin tasirin ayyukan gwamnati kai tsaye a rayuwar jama’a, musamman yadda ake kokarin bunkasa tattalin arziki da samar da yanayi mai kyau ga kasuwanci.
Alhaji Gambo Haruna Yusuf ya yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf addu’ar samun karin lafiya, hikima da karfin guiwa, tare da fatan Allah Ya ba shi nasara a zaɓen 2027, domin ci gaba da hidimtawa al’ummar jihar Kano da kammala manyan ayyukan da ya fara.
Haka zalika, ya yi addu’o’i na musamman ga mahaifiyar Gwamnan Jihar Kano, inda ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ba ta lafiya, tsawon rai da albarka, tare da ci gaba da zuba alheri a cikin rayuwarta.
Ya kammala jawabin nasa da kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da mara wa gwamnati baya, domin samun ci gaba mai ɗorewa da walwala ga kowa da kowa.


