DSS Ta Kama Jami’inta Bisa Zargin Sace Yarinya tare Da Tilasta Mata Sauya Addini
Lamarin ya biyo bayan umarnin da wata kotu da ke Haɗeja, a Jihar Jigawa, ta bayar a makon nan na kamo jami’in domin bincikarsa kan zarge-zargen da ake yi masa game da yarinyar mai shekaru 16.
A cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta DSS, Favour Dozie, ta fitar kuma aka wallafa a shafin hukuma, DSS ta tabbatar da cewa tana gudanar da bincike kan lamarin.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’in da aka kama sunansa Ifeanyi Onyewuenyi, ba Ifeanyi Festus ba kamar yadda umarnin kotu ya nuna.
Hukumar ta DSS ta jaddada cewa zarge-zargen da ake yi wa jami’in sun saɓa wa ƙa’idoji da dokokin aikin hukumar, inda ta sha alwashin bayyana sakamakon binciken ga al’umma da zarar an kammala.
Rahotanni sun nuna cewa jami’in ya sace yarinyar ne kusan shekaru biyu da suka gabata, inda ya ɓoyeta a hannunsa, ya tilasta mata sauya addini zuwa Kiristanci, sannan ya riƙa lalata da ita har ta haihu.




