Political Presenter Forum Ta Yi Jimamin Rasuwar ‘Yan Majalisar Kano Biyu

Ƙungiyar masu gabatar da shirye-shiryen siyasa ta Jihar Kano, wato Political Presenter Forum, ta miƙa sakon ta’aziyya ga al’ummar Jihar Kano bisa rasuwar ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano guda biyu,
Hon Sarki Aliyu Daneji da Hon. Aminu Sa’adu Ungogo.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana rasuwar ‘yan majalisar a matsayin babban rashi ga Jihar Kano, tana mai cewa gudummawar da suka bayar a siyasar jihar ba za a taɓa mantawa da ita ba.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Muhammad Wali, ya miƙa ta’aziyya ga al’ummar Ƙananan Hukumomin Birnin Kano da Ungogo, da Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da kuma Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na II.
Ƙungiyar ta kuma yi addu’a ga Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta wa mamatan, Ya jikansu da rahama, tare da bai wa al’ummar Kano da iyalan mamatan juriyar wannan babban rashi.
Sanarwar ta fito ne ta hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar, Mubarak Auwal Unguwa Uku.




