Labarai

Rundunar ‘yansandan jihar Benuwe ta tabbatar da garkuwa da dukkan fasinjojin wata motar bas ta kamfanin Benue Links a hanyar Eke, Ugbokolo a karamar hukumar Okpokwu ta jihar a yammacin Lahadi.

Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Lahadi, inda wasu ‘yan bindigar suka tare wata motar bas din da ta taho daga Abeokuta, suka yi awon gaba da fasinjojin da ke cikinta bayan sun kwace kayayyakinsu, sannan suka tafi da su cikin daji

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Benuwe, Edet Udeme ya bayyana cewa, lamarin ya rutsa ne da wata motar bas kirar Toyota mai lamba 14B-143BN, wadda aka same ta a gefen titi a Ugbokolo, cikin karamar hukumar Okokwu.

A cewar Udeme, da samun rahoton lamarin, tawagar ‘yansanda tare da hadin gwiwar sojoji da kuma ‘yan sa kai na al’ummar jihar Benuwe, suka yi gaggawar zuwa wurin.

Udeme ya kara da cewa, an tura karin wasu sojoji a yankin domin kara kaimi wajen neman sauran fasinjojin da kuma tabbatar da dawowarsu cikin koshin lafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button