Fadar shugaban tarayyar Najeriya ta ce sai bayan babban taron jam’iyyar ne Shugaba Tinubu zai zaɓi wanda zai zama mataimakinsa a zaɓen shekarar 2027.

Mai bawa shugaba Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanug ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust.
A baya-bayan nan, rashin jituwa na neman ɓullowa a APC kan wanda zai yi wa Tinubu mataimaki, bayan da gwamnonin APC suka amince da shugaban ƙasar a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a 2027.
A ƙarshen mako ne aka kusa bai wa hamata iska a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na shiyyar arewa maso gabas, bayan da wasu ƴan jam’iyyar suka zargi wasu jagorin jam’iyyar da rashin ambatar sunan Kashim Shettima a lokacin da suke jawabin amincewa da Tinubu a matsayin ɗan takarar.
To sai dai tun bayan faruwar lamarin, ba a ji ta bakin fadar shugaban ƙasar ba, lamarin da ya sa wasu ke ganin akwai shirin janye Kashim ɗin daga takarar a 2027.
To amma Bayo Onanuga ya musanta wannan zargi yana mai cewa lokaci ne bai yi ba.



