Ketare
Mutum tara sun mutu a Kyiv a wani mummunan harin sama na Rasha

Aƙalla mutane tara sun mutu kuma da dama sun jikkata a wani harin makami da jirgin sama mara matuki da Rasha ta kai a daren jiya a yankin Kyiv, in ji ministan cikin gida.
A cikin wani sakon da aka wallafa a kafafen sada zumunta, Ihor Klymenko ya ce an kai hari kan wuraren zama, asibitoci da kuma gine-ginen wasanni.
Magajin garin Kyiv Vitali Klitschko ya ce akalla shida daga cikin wadanda suka mutu na cikin wani babban bene a babban birnin kasar. Hukumar soji ta birnin ta ce an kuma jikkata wasu mutane 33.
Shugaba Volodymyr Zelensky yana Kan hanyarsa ta zuwa London a ranar Litinin don tattaunawa da Firaministan birtaniya Keir Starmer kan tallafin soji na Birtaniya ga Ukraine.




