Al’ummar garin Zaria Jihar Kaduna sun yaba ma Kakakin majalisar wakilai Dr. Tajuddeen Abbas bisa jagoranci na gari da kyautatawa al’umma

A yayin gudanar da bikin murnar cika shekaru biyu da saman kujerar shi ne mutane suka haɗu domin tofa albarkacin bakinsu.
Al,ummar mazaɓar zariya sun bayyana Dr Abbas a matsayin wani babban jigo ne ga al’ummar jihar kaduna da ma Nigeria baki ɗaya.
Sun kara da cewa jagorancin sa ya haifar musa da ci gaba ta fannoni da dama ciki harda ilimi, samar wa da al’umma madogara, kiwon lafiya da noma.
Malam Sani daya daga cikin masu yabo da kyautatawar da Kakakin Majalisar yayi musu yana mai cewa ayyukan jin ƙai da na ci gaba da ya aiwatar sun yi tasiri sosai a rayuwar al’ummar mazabar Zariya da sauran sassan jihar Kaduna.
Malam sani yakara da cewa baya cikin jam’iyyar siyasa daya da kakakin, amma hakan bai hanashi halartar taron daya gudana a Zariya ba, ya qara da cewa ya halarci taron domin nuna godiya da yaba masa.
Hakanan shima wani matashin mai suna Zubairu Lawal mutumin Tudun Wada, ɗalibi ne da ya bayyana godiya bisa tsarin tallafin karatu na Kakakin Majalisar da ya basu, inda ya samu tallafi na naira dubu dari biyu da hamsin (₦250,000) domin gudanar da karatunsa cikin salama.
Hakanan Aliyu Dangaladima daga Kufena shima wani manomi ne da ya samu tallafi daga wajan Kakakin majalisar, ya samu takin zamani da kayan noma, wanda hakan ya inganta harkar noma sa, ya shaida wa al’umma cewa tarin manoma sun wadata albarkacin Dr. Tajuddeen Abbas.
Al’umma sun bukaci sauran masu rike da mukaman siyasa da suyi koyi daga irin shugabanci da Dr. Abbas ke yi a wannan zamani na shi mai cike da tarin albarka.
Sun kara bayyana cewa shekaru 14 da ya yi a Majalisar Wakilai sun tabbatar da yadda ya samu amincewa daga jama’a dari bisa dari yadda yake gudanar da aikinsa da kwazo.
Bikin cika shekara biyu da Kakakin ya yi a ofis sun fara gudana ne a ranar Juma’a har zuwa Lahadi.
Wannan biki ya shaida irin jajircewar ga Kakakin Majalisar yayi wajen kula da aikinsa da kuma ƙudurin da ya dauka na ci gaban jama’a da haɗe kan al’umma baki daya cewar Aliyyu Dangaladima.




