Labarai

Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutum 30 sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutum 30 sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a kan al’ummomin Zuru.

Shugabannin Ƙananan Hukumomin Zuru da Danko Wasagu ne suka tabbatar da hakan a wata ziyarar da Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida ya kai Tadurga da Gajere da Bena .

Muhammad Gajere da Hussaini Bena sun bayyana cewa an kashe mutum 16 a Tadurga sai kuma 14 sun rasu a Kyebu da ‘Yar-Kuka da ke gundumar Waje.

Sun kuma bayyana cewa maharan sun tsere da dabbobi da sauran muhimman abubuwa.

Sanata Tafida ya jajanta wa al’ummomin da abin ya shafa waɗanda duka ke ƙarƙashin masarautar Zuru dangane da iftila’in da ya afka musu

Haka kuma mataimakin gwamnan ya bai wa al’ummomin Tadurga da Kyebu naira miliyan 25 kowanensu domin taimaka wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan lokaci.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da matsalar tsaro a Nijeriya musamman matsalar ‘yan fashin daji da kuma mayaƙan Boko Haram.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button