Labarai

Ana sa ran wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Afirka za su halarci jana’izar marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da za a yi yau Talata a mahaifarsa Daura.

Shugabannin ƙasashen sun haɗa da na Gambia Adama Barrow da na Chadi Mahamat Déby da na Guinea Bissau Umaro Sissoco Embaló.

Tsohon shugaban ƙasar Ghana ma Nana Akufo Addo ya yi wa iyalan marigayin ta’aziyya a Landan tun a jiya Litinin kafin gawar ta bar Landan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button