Labarai
Gwamnatin Tarayya ta koka kan karancin cinikayya tsakanin kasashen Afirka, musamman a yammacin Afirka “inda cinikayya tsakanin kasashe ya ragu da kashi 10 cikin 100,” duk da yunkurin hadewa da ake ta faman yi shekara da shekaru.

Ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dr. Jumoke Oduwol, ce ta bayyana haka a taron tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a.
Ta yi gargadin, cewar Kasuwannin Afrika ba za su iya yin girma ba idan suka kasance a wargaje tare da yin kira da a wargaza dukkan shingen harajin da zai iya kawo cikas ga kwararar kayayyaki, ayyuka, da kuma mutane.”
Oduwole ta jaddada rawar da Najeriya ke takawa wajen aiwatar da tsarin yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka, inda ya bayyana cewa a baya-bayan nan kasar ta fitar da jadawalin rangwamen kudin fito na wucin gadi bayan amincewar shugaban kasa.




