Labarai

Jihar Kano Ta Kaddamar da Shirin “Operation Safe Corridor” Don Ƙarfafa Tsaro a Ciki Gida

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani sabon shiri mai suna “Operation Safe Corridor”, wanda yake da nufin tabbatar da zaman lafiya da tsaro ta hanyar sake tarbiyya da gyaran halayen matasa da ke fama da matsalar ‘yan daba a cikin al’umma.

Yayin kaddamar da shirin a ranar Alhamis da ta gabata a dandalin Fele Events Centre da ke Kano, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa wannan shiri wani bangare ne na dabarun da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa domin karkata hankalin matasa daga harkokin tashin hankali da laifuka.

Waiya ya ce: “Yau rana ta uku kenan muna tattaunawa da matasa daga kananan hukumomi takwas na birnin Kano. Akwai dalilin da yasa aka halicce mu, kuma na farko shine bautar Allah. A cikin wannan hanya ne za mu hana mummuna mu kuma karfafa alheri.”

Kwamishinan ya kara da jaddada cewa shirin yana da tushe na addini da ɗabi’a, inda ya ce: “Allah Madaukakin Sarki ya haramta kashe rai da cutar da wani. Kada wani ya umarce ka da cutar da wani mutum. ‘Yan siyasa da ke baku kwayoyi ko makamai ba abokanku bane, makiyanku ne.”

A cewarsa, Gwamnan Jihar Kano yana da kyakkyawan niyya na tallafa wa matasa da kuma basu sabuwar rayuwa. “Gwamnanmu yana da niyyar taimaka muku matasa, shi yasa muka taru daku a nan domin bayyana muku sabuwar dabara ta gwamnati,” in ji shi.

Sai dai kuma ya ja kunne da cewa: “Ba za mu yarda da rashin doka ba. Muna son ku daina aikin ‘yan daba. Idan sun baku kudi, ku karba, amma kada ku yarda ku shiga cikin tashin hankali da suka shiryawa.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button