Bayanan sirri sun nuna cewa harin Amurka bai tarwatsa cibiyoyin nukiliyar Iran ba
Cibiyoyin nukiliyar Iran da Amurka ta jefa wa gagarumin makamin tarwatsa gine-ginen ƙarƙashin ƙasa

Luguden wutar bamabamai da Amurka ta yi a kan tashoshin nukuliya na Iran ba su lalata makamashin nata ba, a cewar wani bincken farko-farko da hukumar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi.
Majiyoyi sun shaida wa kafar yaɗa labarai ta Amurka CBS mai ƙawance da BBC cewa hare-haren na ranar Asabar ba su lalata kayan samar da makamashin na Iran ba, sai dai kawai ƙila sun rage wa Iran hanzari wajen samar da makamin na nukiliya.
Fadar gwamnatin Amurka ta bayyana rahoton da aka kwarmata wa manema labarai da “cikakkiyar ƙarya” da wani “ƙaramin ma’aikaci a ɓangaren tattara bayanan sirri ya fitar”.
Shugaba Trump ya sake nanata cewa hare-haren sun lalata tashoshin nukilyar “gaba ɗaya” kuma ya zargi kafofin yaɗa labarai da “yunƙurin ƙasƙantar da ɗaya daga cikin hare-hare mafiya nasara a tarihi”.
Amurka ta kai wa tashoshin uku hare-hare da suka ƙunshi Fordo, da Natanz, da Isfahan ta hanyar jefa musu bamabaman da ke iya ragargaza ramukan da ke ƙarƙashin ƙasa masu zurfin mita ƙafa 60 na kankare ko kuma ƙafa 200 na ƙasa.
Sai dai majiyoyin da ke da masaniya kan bayanan sirrin na Amurka sun ce akasarin na’urorin sarrafa makamashin da ake kira centrifuges “lafiyarsu ƙalau” kuma iya saman ginin kawai aka lalata – ban da ramukan ƙarƙashin ƙasar.
An toshe wasu hanyoyin shiga tashoshin biyu, kuma an lalata wasu daga cikin kayayyakin, amma akasarin wurin da ke can ƙarƙashin ƙasa ba su ji komai ba.
Bayanan da ba a bayyana wanda ya kwarmata su ba sun ce abin da kawai hare-haren suka cimma shi ne rage wa Iran sauri “na ‘yan watanni”, kuma saurin ma zai danganta ne kan irin gaggawar da Iran ɗin ta yi na lalubo abubuwan da aka binne a ƙarƙashin ƙasar saboda harin.
Wasu majiyoyin sun kuma tabbatar wa CBS cewa Iran ta kwashe wasu daga cikin makamashin uranium da ta sarrafa tun kafin a kai mata hare-haren.
An yi ta tunanin cewa makeken bam ɗin Amurka ) Massive Ordnance Penetrator mai nauyin kilogiram 14,000, shi ne kaɗai ne zai iya tarwatsa masana’antar samar da nukiliyar ta Iran da ke ƙarƙashin ƙasa.
Iran ta sha nanata cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne ba don yaƙi ba.
‘Yan awanni bayan kai harin na ranar Asabar, shugaban majalisar rundunonin tsaron Amurka Janar Dan Caine ya faɗa wa manema labarai cewa za a ɗauki lokaci kafin tabbatar da abin da ya faru a wurin harin.
Amma ya nanata cewa “duka tashoshin uku an tarwatsa su sosai”. Hotunan tauraron ɗan’adam sun nuna ramuka shida sababbi a kusa da mashigar ramuka biyu na Fordo, da ƙura da kuma ɓaraguzai.
Ba za a iya tabbatar da komai ba daga hotunan, ballantana kuma irin ɓarnar da bama-baman suka yi a ƙarƙashin ƙasar.
Hassan Abedini, mataimakin shugaban sashen siyasa na kafar yaɗa labaran gwamnatin Iran ya ce na kwashe kayayyaki daga tashoshin uku “babu daɗewa” kuma Iran “ba ta yi wata asara mai yawa ba saboda tuni aka kwashe kayan.”
A gefe guda kuma, jami’an gwamnatin Amurka na ta yabon nasarar hare-haren kamar takwarorinsu na Isra’ila.
Cikin wata sanarwa a ranar Talata, Sakataren Tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce “bisa ga abubuwan da muka gani – kuma na ga komai da komai – hare-harenmu sun tarwatsa ikon Iran na ƙera makaman nukiliya”.
“Duk wanda y ace bama-baman ba su yi aiki da kyau ba kawai yana so ne ya yi wa shugaban ƙasa zagon ƙasa da kuma nasarar aikin,” in ji Hegseth.
Ɗanmajalisar wakilan Amurka Brad Sherman na jam’iyyar adawa ta Democrat kuma mamba a kwamatin harkokin waje ya faɗa wa BBC cewa gwamnatin Trump na amfani da kalamai marasa cikakkiyar ma’ana wajen ayyana nasara – bayan kuma har yanzu babu tabbas kana bin da harin ya cimma.
“Idan suka ce sun tarwatsa Shirin na Iran, ba su bayyana ko suna nufin lalata na’urorin centripuges da kuma damar ci gaba da sarrafa uranium nan gaba, ko kuma suna nufin tarwatsa makamashi da aka riga aka samar,” a cewar Sherman.
“Dukkan abubuwa, ciki har da kalaman Mataimakin Shugaban Ƙasa Vance, na nuna cewa ba mu tarwatsa sarrafaffen makamashin ba,” in ji shi.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya faɗa ranar Talata cewa suns amu nasarar daƙile yunƙurin Iran ɗin na samun nukiliya tun bayan fara kai wa juna hare-hare ranar 13 ga watan Yuni, ciki har da lalata makamanta masu linzami.
“Mun kawar da barazana biyu daga kanmu – barazanar harin nukiliya da kuma ta makamai masu linzami 20,000 na Iran,” a cewar Netanyahu cikin wani saƙon bidiyo.
Wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Saudiyya Al Hadath ta wallafa ya Ambato wata majiya daga Isra’ila na cewa sun yi imanin an binne mafi yawan makamashin da Iran ta riga sarrafa a ƙarƙashin ɓaraguzai.
Amurka na da hukumomin leƙen asiri 18, waɗanda a wasu lokutan ke fitar da rahotonni masu cin karo da juna bisa ga fahimtarsu da kuma ɓangaren da suke lura da shi. Misali, har yanzu hukumomin sun kasa cimma matsaya kan inda cutar Korona ta samo asali.
Akwai yiwuwar a samu wasu bayanan nan gaba da za su bayar da ƙarin masaniya kan al’amarin.
A ranar Litinin Iran ta kai harin ramuwa kan sansanin Amurka na Al-Udeid da ke Qatar. An kakkaɓe akasarin makaman kuma babu wanda ya ji Rauni.
Tun bayan ramuwar ta Iran, an samutsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran wadda har yanzu take aiki.




