Manufar Trump a Afirka ka iya zama mai amfani ko illa
manufar sojin Amurka a kan Afirka na sauyawa a karkashin gwamnatin Trump

Irin yadda Shugaban Amurka Donald Trump ya dukufa zaftare yawan kudaden da kasar ke kashewa tun bayan da ya sake darewa kan mulki a karo na biyu, ya rage yawan tallafin da kasar ke ba Afirka, kuma yanzu ya sa ido a kan harkar tsaro – to amma ko wannan mataki zai iya yin karin wata illar a nan gaba.
Matakin da Shugaban ya dauka na sa kasashen Turai su dauki nauyin harkokin tsaronsu, shi ne kuma gwamnatinsa ke sa kasashen Afirka su ma su yi hakan a yanzu, to amma hakan ko lama bai yi wa kasashen na Afirka dadi ba.
Ganin irin yadda kasashen na Afirka suka himmatu wajen kashe dukiya da sadaukar da rayukan sojojinsu wajen yakar kungiyoyin masu ikirarin jihadi a fadin yankin Sahel da yankin tafkin Chadi da Somalia a shekarun nan, ba kawai domin al’ummominsu ba, har ma da nahiyar gaba daya, to za a iya cewa lalle sa nuna damuwa a kan wannan aniya ta Amurka.
jamhuriyar Benin wadda ta rasa sojoji sama da 80 a wani hari na kungiyoyin masu ikirarin jihadi tun daga farkon shekaran nan daya ce daga cikin irin wadannan misalai.
”Cibiyar ayyukan ta’addanci ta duniya” shi ne yadda a kwanakin baya Janar Micheal Langley kwamandan rundunar sojin Amurka a yankin Afirka (Africom) a kudu da hamadar Sahara ya bayyana yankin Sahel.




