Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Umurci Fitar da ‘Yan Najeriya daga Isra’ila da Iran

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umurnin gaggawa na fitar da ‘yan Najeriya daga kasashen Isra’ila da Iran, sakamakon ƙarin tsanani da rikici da ke tsakanin kasashen biyu na Gabas ta Tsakiya.

Wannan umurnin na fitar da ‘yan kasa ya biyo bayan barkewar hare-haren soja, inda Isra’ila ta kaddamar da luguden wuta a manyan wurare fiye da 100 a Iran tun daga ranar Juma’a, ciki har da wuraren soja da na nukiliya.

Rahotanni sun ce harin ya hallaka manyan jami’an sojin Iran da dama, wanda hakan ya haifar da mayar da martani cikin gaggawa daga Iran, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama na fararen hula da na soja a bangarorin biyu.

A sakamakon tabarbarewar tsaro, Ma’aikatar Harkokin Waje ta sanar da cewa tana cikin shirye-shiryen fitar da ‘yan Najeriya da suka makale a kasashen biyu.

“Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da cewa, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin kasar Isra’ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Gwamnatin Tarayya na kammala shirye-shirye don fitar da ‘yan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali a wadannan kasashe,” in ji mai magana da yawun ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, a daren Talata.

Ma’aikatar ta kuma shawarci dukkan ‘yan Najeriya da ke cikin Isra’ila da Iran da su kiyaye dokokin tsaro na kasashen da suke ciki, tare da tuntubar ofishin jakadanci ko wakilcin Najeriya mafi kusa da su nan da nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button