FRSC Ta Sallami Jami’ai 43 Bisa Rashin Biyayya da nuna Ɗabi’a Maras Kyau

Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗura ta Ƙasa (FRSC) ta ɗauki matakin ladabtarwa mai tsauri inda ta sallami jami’ai 43 daga aiki sakamakon laifuka daban-daban da suka aikata yayin gudanar da ayyukansu.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa daga cikin jami’an da aka sallama, 31 an kore su ne saboda rashin biyayya, biyar kuma saboda ɗabi’a maras kyau, yayin da bakwai aka sallame su saboda aikata laifuka a lokacin sintiri.
Shugaban FRSC, Shehu Mohammed, ya bayyana matakin a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da cewa jami’ai suna bin ƙa’idojin aiki yadda ya kamata tare da kare martabar hukumar.
Ya ce, “Alamar FRSC alama ce ta ɗabi’a da ɗawainiya, kuma kowane jami’in da ya saba wa ƙa’idojin hukumar zai fuskanci hukunci.”
Shugaban ya ƙara da cewa rashin biyayya babban laifi ne, musamman ga hukuma da aka ɗora wa alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a kan hanyoyi.
Ya kuma jaddada cewa ɗabi’a maras kyau da aikata laifuka yayin sintiri na rage amincewar jama’a ga hukumar tare da saba wa ƙa’idojin gaskiya da ladabi.
Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin sa ido da kulawa a cikin gida, tare da wayar da kan jami’ai kan muhimmancin ɗabi’a mai kyau da bin ƙa’idoji a dukkan sassan hukumar a faɗin ƙasa.




