Labarai

Ma’aikatan FCTA Sun Garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin NIC da Ya Umurce Su Komawa Aiki

Ma’aikatan Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya (FCTA) kimanin 40,000 sun garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar hukuncin Kotun Kwadago ta Ƙasa (NIC) da ta umurce su da su dakatar da yajin aiki su koma bakin aiki.

Ma’aikatan sun shiga yajin aikin na dindindin bayan rushewar tattaunawa da mahukuntan FCTA kan buƙatunsu 18, ciki har da rashin ƙarin girma, bashin Wage Award na 2023, rashin tura kuɗin fansho zuwa asusun ritaya, da rashin horo.

Kotun NIC ta ce yajin aikin bai halatta ba tun da shari’ar ta riga ta je gaban kotu, inda ta bayar da umarnin komawa aiki domin hana durƙushewar ayyukan gwamnati a Abuja.

Sai dai NLC ta soki hukuncin, yayin da ma’aikatan suka ƙi komawa aiki, suna mai jaddada cewa ba za su daina yajin aikin ba har sai an biya musu dukkan buƙatunsu.

 

A yanzu haka, shari’ar na gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara, inda ƙungiyoyin ma’aikatan ke neman dakatar da aiwatar da hukuncin NIC har zuwa kammala sauraron ƙarar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button