Labarai

NAFDAC Ta Ƙwace Magungunan Zazzaɓin Cizon Sauro na Bogi na Miliyan 10 a Lagos

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta sanar da ƙwace sama da magungunan zazzaɓin cizon sauro na bogi na miliyan 10, tare da kayan kwalliya, waɗanda kimarsu ta kai kusan naira biliyan uku, a wani gagarumin farmaki da ta kai kasuwar baje koli a jihar Lagos.

 

Daraktan bincike da aiwatar da doka na hukumar, Dr. Martins Iluyomade, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin NAFDAC da ke Apapa, a ranar Litinin.

A cewarsa, an kai farmakin ne ƙarƙashin jagorancin shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, bayan da hukumar ta samu sahihan bayanan sirri a ranar 3 ga Fabrairu.

Dr. Iluyomade ya ce kayayyakin da aka ƙwace sun haɗa da magungunan yaƙi da zazzaɓin cizon sauro, alluran cutar cerebral malaria, magungunan rigakafi, maganin tazarar haihuwa na Postinor, da Anagin, dukkansu na bogi ne.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin magungunan da aka samu an haramta amfani da su a Najeriya tun kusan shekaru 15 da suka wuce, saboda illolin da suke haifarwa ga lafiyar jama’a.

Daraktan ya bayyana cewa an adana magungunan bogin ne a cikin wani gini mai hawa uku da aka ɓoye shi a matsayin sito na kayan gyaran mota, domin yaudarar jami’an tsaro da sauran hukumomi.

A yayin farmakin, jami’an NAFDAC sun kwashe lodin manyan motoci guda takwas na magunguna da kayan kwalliya, tare da kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a wannan haramtacciyar sana’a.

Dr. Iluyomade ya ce bincike na ci gaba da gudana, yana mai bayyana farmakin a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da NAFDAC ta samu a baya-bayan nan wajen yaƙi da yaɗuwar magungunan bogi a Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button