Labarai

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutum 32, a Wani Hari da suka kai a Jihar Kaduna

Ana fargabar wasu ƴan bindiga sun yi awon-gaba da mutum 32, ciki har da ƙananan yara, tare da kashe mutum ɗaya a wani mummunan hari da suka kai garin Kadagen Kauru da ke Ƙaramar Hukumar Kauru a Jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne a daren Litinin, inda mazauna garin suka tsinci kansu cikin firgici yayin da maharan suka afka cikin al’umma ba tare da shiri ba.

 

Harin na zuwa ne kasa da wata guda bayan wani makamancin sa da aka kai a garin Kabari, wanda ke makwabtaka da Kadagen Kauru, inda ake zargin ƴan bindiga sun sace mutum 85.

 

Wannan ya biyo bayan jerin hare-haren da aka rika kaiwa wasu ƙauyuka a yankin, lamarin da ke ƙara tayar da hankula a tsakanin al’umma kamar yadda Dala fm ta rawaito

 

Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa har yanzu ana cikin jimami da tashin hankali sakamakon sace mutanen da aka yi, yayin da iyalai ke ci gaba da neman bayani kan makomar ’yan uwansu da aka yi awon-gaba da su.

 

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, sai dai al’umma na kira ga gwamnati da ta ƙara tsaurara matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button