Ana Shirin Zanga-zangar Neman Hakkin Iyalan Mafarautan Kano Da Aka Yiwa Kisan Gilla A Edo

Iyalan Mafarautan Kano da aka yiwa kisan gilla su 16 a Jihar Edo, sun bukaci gwamnatin Jihar Kano da takwararta ta Jihar Edo da su tabbatar da an yiwa ‘yan uwansu da iyalansu Adalci gami da biyan harkokin da aka yi musu Alkawari.
Idan za’a iya tunawa a watan Afirilun 2025 ne gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da gwamnan Jihar Edo Sanata Monday Okpebholo suka ziyarci ‘yan uwan wadanda aka yiwa Kisan Gillar a garin Uromi na Jihar Edo cikin watan Maris na 2025 inda a yayin ziyarar suka yi Alkawarin biyan diyya ga iyalan Mafarautan da suka fito daga kananan hukumomi biyar wadanda suka hada da Bunkure, Garko, Dawakin Kudi, Kibiya da kuma Rano.
To amma, a tattaunawarsa da GLOBAL TRACKER, Shugaban kwamitin ‘iyalan wadanda aka kashewa ‘yan uwa Malam Haruna Iliyasu Kibiya ya ce har ya zuwa yanzu sama da watanni 8 babu wanda aka biya koda sisin Kobo.
Ya ce iyalai da yawa sun fada mawuyacin Hali na rashin samun wani tallafi mai dorewa lamarin da ya jefa su cikin bakar wahala sakamakon rashin magidantansu da suka yi.
“Iyalan Mafarautan nan da aka kashe suna cikin kunchi da Talauci ko abinci ba su da shi, ‘ya’yan su basa iya zuwa makaranta, muhallinsu duk ya lalace saboda babu magidantan, wannan abu yana mana ciwo, yakamata gwamnatin Jihar Kano da Jihar Edo su cika Alkawarin da suka dauka,” inji Haruna Kibiya.
A wani cigaban labarin kuma, gamayyar kungiyoyin dake rajin kare yankin Arewacin Nigeriya da ma al’umma yankin ta ce shirye-shirye sunyi nisa domin gudanar da zanga-zangar lumana da nufin neman mahukunta su biya diyya gami da daukar nauyin iyalan wadanda aka kashe kamar yadda gwamnan Kano da na Edo suka yi Alkawari.
Sakataren gamayyar kungiyoyin kwamared Kabiru Sani Garko ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da GLOBAL TRACKER inda ya ce zasu gudanar da zanga-zangar ne a Birnin tarayya Abuja cikin mako na biyu na watan Fabarairu, 2026 mai zuwa don neman hakkin iyalan Mafarautan na Kano.
Ya yi fatan al’ummar Nigeriya za su goya musu baya don cimma nasarar da aka sanya a gaba.



