Labarai

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da cibiyar Fasaha ta Zamani ta Arewa maso Yamma da hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta gina a Kano, wadda matasa suka lalata a lokacin zanga-zangar ƙuncin rayuwa ta #EndBadGovernance a watan Agustan 2024.

Ministan Harkokin Sadarwa Dr. Bosun Tijani, ne ya wakilci shugaban ƙasa a wajen bikin ƙaddamarwar.

A jawabin sa, Minista Tijani ya bayyana cewa wannan katafaren aiki da gwamnatin Tinubu ta samar ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda, zai iya zama babbar hanya ga matasa su tsira daga talauci idan har suka yi amfani da damar yadda ya kamata.

Ya bayyana damuwarsa kan lalata cibiyar mako guda kafin a ƙaddamar da ita, duk da cewa an kammala aikin tun watan Janairu.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ta bakin mataimakinsa Abdussalam Gwarzo, ya ce jihar na da shirin horas da matasa 300,000 kan fasahar zamani nan da shekarar 2027.

Ya bayyana cewa tuni aka fara horar da ma’aikatan gwamnati 5,000 da suka samu ƙwarewa a fannin fasaha.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button