Barakar Siyasa Ta Bayyana Tsakanin Gwamna Abba da Kwankwaso a Kano

A daidai lokacin da raɗe-raɗen sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC ke ci gaba da ɗaukar hankali a jihar Kano, wata sabuwar ɓaraka ta bayyana, wacce ke nuna akwai tsamin dangantaka tsakanin gwamnan da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Wannan alamar tsamin dangantaka ta fito fili ne a ƙarshen makon da ya gabata, lokacin da wasu manyan magoya bayan Sanata Kwankwaso suka ƙaurace wa wani muhimmin taron yaye ɗaliban da suka koyi sana’o’in hannu.
Gwamna Abba ne ya jagoranci taron a fadar gwamnatin jihar, kuma rashin ganin fuskokin fitattun ‘yan Kwankwasiyya a wurin ya haifar da tambayoyi masu yawa game da yanayin alaƙar da ke tsakaninsu.
Abin lura shi ne, wannan taro shi ne karo na farko da aka ga Gwamna Abba a bainar jama’a bayan shafe fiye da mako guda ba tare da fitowa fili ba.
Daga cikin waɗanda ba su halarci taron ba akwai Hashim Sulaiman Dungurawa, wanda aka sani a matsayin makusancin Sanata Kwankwaso. Haka kuma, wasu kwamishinoni da manyan jami’an gwamnati da ake ganin makusantan Kwankwaso sun haɗa da Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso; Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dr. Yusuf Kofar Mata; Kwamishinan Tsaro na Kano, AVM Ibrahim Umar mai ritaya; tare da Shugaban Ma’aikata, Abdullahi Musa.
Sai dai kuma, a wurin taron, an ga sabon shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Abdullahi Zubairu Abiya, yana halarta, wanda hakan ya ƙara nuna canjin yanayi a cikin jam’iyyar da gwamnatin jihar
Wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan makomar siyasar jihar Kano da kuma tasirin Sanata Kwankwaso a cikin gwamnatin Gwamna Abba.




