Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano Ta Horar da Direbobinta Kan Sanin Ka’idojin Tuƙi

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta shirya wani muhimmin taron horo, irinsa na farko, domin horar da direbobinta, da nufin ƙara musu fahimta kan ka’idojin tuƙi cikin nutsuwa, bin doka da oda, da kuma kyakkyawar mu’amala a yayin gudanar da aikinsu.
Taron horon ya mayar da hankali ne kan koyar da direbobi muhimmancin bin dokokin hanya, kare rayuka da dukiyoyi, da mutunta shugabannin da suke yi wa aiki, domin inganta aikin gwamnati da rage haɗurra.
A yayin taron, an gabatar da laccoci da jawabai daga manyan jami’ai a fannoni daban-daban, inda aka jaddada muhimmancin ladabi, ɗabi’ar aiki, da bin ƙa’idoji a aikin direba.
Da yake gabatar da jawabi, Babban Sakatare na Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-Ƙirƙire, Alhaji Abba Adamu Danguguwa, ya bayyana cewa tsari da kyakkyawar mu’amala tsakanin direba da wanda yake yi wa aiki na da matuƙar muhimmanci wajen samun nasarar aiki da ingancin hidima.
Haka kuma, Daraktan a Ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Tukur Jalal, ya gabatar da takarda kan matakan da ake bi wajen ladabtar da ma’aikaci idan ya aikata laifi, inda ya bayyana dokoki da ƙa’idojin da suka shafi ladabtarwa ga ma’aikatan gwamnati.
A nasa ɓangaren, Babban Darakta na Cibiyar Horar da Harkokin Tuƙi ta Jihar Kano, Alhaji Garba Abdu Gaya, ya gabatar da jawabi kan yadda ya dace direba ya tuka mota a kan hanya, tare da muhimmancin sanin alamomin tuƙi, domin gujewa haɗurra.
A jawabin rufe taron, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, ta bakin Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya, Pharmacist Aminu Bashir, ya jaddada cewa wannan horo shi ne irinsa na farko da aka shirya musamman domin direbobin Ma’aikatar Lafiya, tare da kira ga mahalarta da su tabbatar sun yi aiki da duk abin da suka koya domin inganta aikinsu da kare martabar Ma’aikatar.
A nasa jawabin, wanda ya yi magana a madadin direbobin, Malam Auwalu Ya’u Karefa, ya bayyana godiyarsu ga Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano bisa ba su damar halartar wannan horo, tare da ba da tabbacin za su yi aiki da duk abin da suka koya a yayin




