Likitoci Masu Neman Ƙwarewa na Asibitin Aminu Kano Za Su Koma Yajin Aiki a Ranar Litinin

Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta reshen Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (ARD AKTH) ta umarci mambobinta da su koma yajin aikin sai baba-ta-gani da ta dakatar a baya. Matakin ya biyo bayan gazawar Gwamnatin Tarayya wajen magance matsalolin da likitocin ke fuskanta a faɗin ƙasar.
Shugaban ƙungiyar na reshen AKTH, Dakta Aminu Bello Aminu, ya bayyana cewa bayan tattaunawa mai zurfi kuma bisa umarnin ƙungiyar likitoci ta ƙasa (NARD), reshen na AKTH ya yanke shawarar shiga yajin aikin gama-gari, wanda ba a san ranar da za a daina ba.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Kano, Dakta Aminu ya ce yajin aikin zai fara ne daga ƙarfe 12 na daren ranar Litinin, 12 ga watan Janairun 2026.
Ya yi bayanin cewa ba a ɗauki wannan matakin da wasa ba. An yanke shawarar ne bayan doguwar tattaunawa, alƙawura da dama da ba a cika ba, da kuma gazawar hukumomin da abin ya shafa wajen magance muhimman matsaloli da suka shafi jin daɗin likitoci, horar da su, da kuma albashinsu, waɗanda ke shafar tsarin kiwon lafiya baki ɗaya.
Shugaban ya bayyana cewa buƙatunsu, waɗanda suka daɗe suna nema, sun haɗa da:
* Maido da likitoci biyar na Asibitin Tarayya na Lokoja (FTH Lokoja Five) bakin aiki nan take.
* Biyan duk wasu basussukan ƙarin girma da na albashi da ake binsu.
* Fara aiwatar da sabon tsarin alawus na ƙwarewa, tare da sanya basussukan a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.
* Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta ba da cikakken bayani ga shugabannin asibitoci kan batun tsallake matakin albashi (skipping) da matsayin fara aiki.



