’Yan sanda sun kama manyan jagororin ’yan fashi biyu a Jihar Kwara

Rundunar ’Yan Sanda ta kama wasu fitattun jagororin ’yan fashi da garkuwa da mutane biyu da ake zargin suna da hannu a manyan laifuka a jihohin Katsina, Zamfara, Niger da Kwara.
A cewar wata sanarwa daga rundunar, an kama su ne a ranar Juma’a, 19 ga Disamban 2025, yayin wani sumamen sirri da jami’an sashen Force Intelligence Department–Intelligence Response Team (FID–IRT) suka gudanar tare da hadin gwiwar rundunar ’yan sandan Jihar Kwara, a yankin Komen–Masallaci da ke Karamar Hukumar Kaiama.
Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai sabon babur Honda Ace 125 mai kimanin kudi naira miliyan 1.85, da kudi naira 500,000 da ake zargin kudin fansa ne, da kuma bindigar AK-47 mai harsashi 20 a cikin ma’aji.
Binciken farko ya nuna cewa mutanen na daga cikin wata kungiyar ’yan fashi da ke addabar al’umma a jihohi hudu, tare da safarar makamai ga masu aikata laifuka.
Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya yaba wa jami’an bisa kwarewa da jajircewa, yana mai jaddada kudirin rundunar na yaki da miyagun laifuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma kamar yadda Gidan talabin na kada N T A ya bayyana a shafin na sada zumunta




