Labarai

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Kano, AVM Ibrahim Umar (Rtd), Ya Yi Murabus

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, Air Vice Marshal Ibrahim Umar (Mai ritaya), ya ajiye aikinsa nan take.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a cikin wasiƙar murabus da ya aika wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda aka kuma aikewa da kwafinta ga kafar yaɗa labarai ta GLOBAL TRACKER a Kano, a ranar Litinin.

A cewar AVM Ibrahim Umar (Rtd), ya ɗauki wannan mataki ne sakamakon tsamin dangantaka da ta shiga tsakanin Gwamnan Jihar Kano da jagoransa na siyasa, Injiniya Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso.

A cikin wasiƙar, ya ce:

“Ina rubuto wannan wasiƙa ne cike da godiya da kuma sanin nauyin da ke kaina domin miƙa murabus na daga muƙamin Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, nan take. Ina miƙa godiya ta ga Mai Girma Gwamna bisa amincewa da ya yi da ni.”

Ya tuno da yadda gwamnan ya fara naɗa shi a matsayin Daraktan Janar na Hukumar Ayyuka na Musamman a watan Yuni 2023, sannan daga bisani aka ɗaga shi zuwa matsayin Kwamishina, yana mai cewa babban abin alfahari ne a gare shi samun damar jagorantar harkokin tsaro a jihar Kano.

Sai dai ya bayyana cewa, la’akari da sabbin abubuwan da suka faru a siyasar jihar, ya ga dacewar ya fice daga muƙamin domin amfanin jihar da kuma gwamnatin baki ɗaya, duk da cewa matakin ya zo masa da wuya.

AVM Ibrahim Umar (Rtd) ya jaddada cewa duk ayyukansa sun kasance bisa turarar jagora da koyarwar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Tafiyar Kwankwasiyya, wadda ke gina adalci, ladabi da hidima ga al’umma.

Ya nuna godiya bisa damar da aka ba shi ta bayar da tasa gudunmawa wajen tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano, tare da tabbatar da cewa zai ci gaba da goyon bayan gwamnati da al’ummar jihar Kano domin samun Kano mai tsaro, ƙarfi da wadata.

A ƙarshe, ya yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf addu’ar samun hikima, ƙarfi da lafiya yayin da yake jagorantar harkokin jihar, tare da roƙon Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) Ya albarkaci Jihar Kano da Tarayyar Najeriya baki ɗaya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button